Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana yau Alhamis ranar 5 ga wata, cewar bisa sanarwa mai lamba 5 ta shekarar 2018, wadda kwamitin kula da ka'idojin haraji na majalisar gudanarwar Sin ya fitar, kasar za ta aiwatar da matakin kara karbar yawan haraji kan wasu kayayyakin Amurka da za su shiga cikin kasuwannin Sin, bayan Amurka ta fara daukar matakan kara yawan haraji kan kayayyakin Sin a hukumance.
Wani mai kula da aikin karbar haraji na babbar hukumar kwastam ta Sin ya bayyana hakan, yayin da yake amsa tambayar da kafofin watsa labarai suka yi, game da lokacin daukar matakan mayar da martani kan kara karbar harajin da Amurka za ta yi wa Sin.(Kande Gao)