Gao Feng wanda ya bayyana hakan Alhamis din nan yayin taron manema labarai, ya ce Amurka ta yi barazanar kakabawa dukkan kayayyakin da kasar Sin take shigarwa cikin kasar wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 500, sannan ta aikewa wasu abokan cinikayyarta irin wannan barazana.
Gao ya ce, kasar Sin ba za ta ji tsoron barazana ko neman shafa mata kashin kaji ba, kana babu wanda zai kawo illa ga harkokin cinikayyar kasa da kasa cikin 'yanci da kasancewar bangarori daban-daban.
Bugu da kari, kasar Sin za ta hada kai da sauran kasashe don yakar masu neman mayar da hannun agogo baya, da tsohon tsari da masu kokarin ba da kariya ga harkokin cinikayya da kasancewar bangarori daban-daban. Haka kuma za ta yi kokarin samar da yanayin tattalin arzikin da harkokin cinikayya da duniya ke fatan gani. (Ibrahim)