Mutane akalla 34 ne suka mutu, wasu 18 kuma suka jikkata, biyo bayan wasu tagwayen hare-hare da aka kai garin Damboa na jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.
Wani jami'in karamar hukumar da ya nemi a boye sunansa, ya ce bayan tagwayen hare-haren, an kuma kai wani harin gurneti kan mutanen da suka je taimakawa wadanda harin farkon ya rutsa da su.
Yankin karamar hukumar Damboa na da nisan kilomita 88 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Jami'in ya kara da cewa, an kai hare-haren ne yayin da mazauna garin ke komawa gida daga kallon gasar kwallon kafa na cin kofin duniya na bana da aka yi tsakanin Nijeriya da Croatia. (Fa'iza Mustapha)