in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da gidaje 100 ne guguwar ruwan sama ta lalata a jihar Katsina
2018-07-03 09:48:45 cri

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN, ya ruwaito cewa, mutum 1 ya mutu, sannan gidaje dari sun lalace sanadiyyar guguwar ruwan sama da aka yi a Dauran jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar, wanda kuma ya kasance mahaifar shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Mutane 4 ne suka jikkata inda suke kwance a asibiti, bayan aukuwar lamarin da yammacin ranar Lahadin da ta gabata.

Makamancin al'amarin ya auku a baya-bayan nan, inda ya raba sama da mutane 600 da matsugunansu a yankin, al'amarin da ya sa shugaban kasar Muhammadu Buhari kai ziyarar yini 2 jihar a ranar Juma'ar da ta gabata domin jajantawa wadanda ibtila'in ya shafa.

Wasu jami'ai dake yankin, sun ce ruwan da aka shafe sa'o'i 8 ana yi a garin Daura, ya yi mummunan barna.

A cewar Aminu Waziri, shugaban hukumar kai agajin gaggawa ta jihar, sama da yankuna hudu na garin Daura ne guguwar ruwan ta shafa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China