in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akalla mutane 10 ne aka kashe a wani hari a arewacin Najeriya
2018-06-14 09:22:11 cri

Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 10 a wani sabon hari da aka kaddamar a shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Akwai kuma mutane da dama da aka jikkata a lokacin da 'yan bindigar suka kaddamar da harin a wasu kauyuka biyu a jihar Zamfara da yammacin ranar Talata.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Zamfara Muhammadu Shehu, ya shedawa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar cewa, jami'an tsaro sun kaiwa kauyukan dauki cikin gaggawa bayan da suka samu rahoton kaddamar da harin daga mazauna kauyukan Dutsen-Wake da Oho dake karamar hukumar Birnin-Magaji a jihar ta Zamfara, inda maharan suka kaddamar da hare haren.

Shehu ya ce, daga bisani 'yan bindigar sun tsere zuwa dajin Rugu wanda ke kan iyakar jihohin Zamfara da Katsina dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Ya kara da cewa, 'yan sandan sun farwa maharan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China