in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin kasashen waje sun fi son gabatar da kara game da tabbatar da ikon mallakar ilmi a kasar Sin
2018-07-02 15:46:09 cri
A sakamakon hukuncin da ake yankewa bisa adalci, kamfanonin kasashen waje sun fi son gabatar da kara game da tabbatar da ikon mallakar ilmi a kasar Sin a shekarun baya bayan nan, kamfanonin kasashen waje 65 sun cimma nasara a kararrakin da suka shigar na sauran kamfanonin kasa da kasa a kotun kare ikon mallakar ilmi a birnin Beijing a shekarar 2015.

Karin kamfanonin kasashen waje sun zabi kasar Sin don gabatar da kararsu a fannin tabbatar da ikon mallakar ilmi, wannan ya shaida cewa, sun amince da nuna imani ga tsarin tabbatar da ikon mallakar ilmi na kasar Sin.

Gwamnatin kasar Amurka sun tada yakin ciniki da kasar Sin a dalilin rashin tabbatar da ikon mallakar ilmi a kasar Sin, burinta shi ne hana bunkasuwar kimiyya da fasaha da tattalin arzikin kasar Sin. Game da yakin ciniki da za a fara, Sin ba ta son yin yakin, kana ba ta jin tsoron yin yakin, tilas ne za ta mayar da martani. Haka zalika kuma, Sin za ta ci gaba da tabbatar da ikon mallakar ilmi, tare da ci gaba da samun bunkasuwa a fannin kimiyya da fasaha. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China