in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin WTO: Hana ciniki ba zai taimakawa samar da guraben aikin yi ba
2018-07-02 11:13:37 cri

Kakakin kungiyar ciniki ta duniya WTO, Keith Rockwell, ya yi hira da wakilin CRI a kwanakin baya, inda ya ce, matakin da wasu kasashe suka dauka na hana ciniki, ba zai taimakawa kokarin samar da karin guraben ayyukan yi a gidansu ba. Kwanan baya, ana ganin alamu na tsanantar yakin cinikin da kasar Amurka take yi ga kasar Sin, da kungiyar tarayyar Turai EU, gami da sauran manyan tattalin arziki, musamman ma a fannin cinikayya. Keith Rockwell, kakakin kungiyar ciniki ta duniya WTO, ya yi amfani da kalmomin "halin dar-dar" da "matsin lamba", wajen bayyana yanayin da cinikin kasa da kasa ke ciki a halin yanzu.

A ganinsa, an fara samun wannan yanayi ne tun daga shekarar 2008, lokacin da aka fama da rikicin hada-hadar kudi a wurare daban daban na duniya. Wancan rikici ya sa ana rasa guraben aikin yi, ya kuma saka damuwa cikin zukatan mutane kan makomarsu. Wannan damuwa ta sa wasu ke ganin cewa, ciniki na kasa da kasa ne ya kwaci guraben aikin yi daga wasu wurare. Amma Mista Rockwell bai yarda da wannan ra'ayi ba, inda ya ce hakika ci gaban da aka samu game da wasu sabbin fasahohin da suka hada da na'urori masu amfani da fasaha da kansu (AI), da fasahar sanya injuna su sarrafa kansu, sun haddasa raguwar guraben aikin yi. Wannan, in ji shi, ba wani abun da za a iya magancewa ba ne.

"Matakin hana ciniki ba zai yi amfani ba. Domin ba zai iya dawo da guraben aiki ba, maimakon haka zai haddasa yanayin na damuwa a wasu bangarori na tattalin arziki. Saboda haka, hanya mafi kyau da za a iya bi wajen daidaita huldar tattalin arziki da cinikayya ita ce zama a teburin shawarwari."

An ce, yanzu a duniyar mu akwai wani tsarin daidaita sabanin ra'ayi wanda ya kasance a karkashin inuwar kungiyar WTO. An samar da wannan tsari ne bisa ka'idojin kungiyar WTO, da yadda ake aiwatar da ka'idojin cikin shekaru fiye da goma da suka wuce domin daidaita sabanin ra'ayi a fannin cinikin kasa da kasa. Ana kallon tsarin a matsayin ginshikin tsarin ciniki da ya shafi bangarori daban daban, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman karko na tattalin arzikin duniya. Tsarin da ya bukaci masu sabanin ra'ayi da su magance daukar matakin radin kai, maimakon haka su bi wasu matakai na daidaita sabanin ra'ayi, sa'an nan su aikata bisa yadda aka yanke hukunci. Sai dai a wannan karo, wasu matakan da kasar Amurka take dauka, ko da yake ta yi musu ado, amma a hakika su ne matakai na kashin kai, wadanda suka sabawa ka'idojin kungiyar WTO.

Shi Keith Rockwell ya amince cewa, tsarin daidaita sabanin ra'ayi na kungiyar WTO shi ma yana tare da wasu matsaloli, abin da ya sa wasu mambobin kungiyar, ciki har da Amurka, da Sin, da kungiyar EU, ke neman yin kwaskwarima kan tsarin. Shi babban sakataren kungiyar WTO, Roberto Azevedo, shi ma ya ce, ka'idojin kungiyar da dama na cikin yanayi na koma baya, wadanda ke bukatar gyaranbawul don dace da yanayin zaman al'umma na yanzu. Sai dai daukar gyare-gyaren na bukatar lokaci, kana ainihin bayanan da za a gyara na bukatar bangarori su tattauna a kai. Amma wata babbar matsala da ake fuskantar yanzu ita ce yadda kasar Amurka take kokarin hana hukumar kai kara ta kungiyar WTO ta gudanar da aikinta.

"Kasar Amurka ta nuna shakku kan yadda ake gudanar da ayyukan hukumar karbar kara dake karkashin kungiyar WTO, don haka take hana hukumar aikin ta. Kasar Amurka ta dade tana nuna shakku, amma muna bukatar ta bayyana ainihin abubuwan da take so, ta yadda za a iya zama a teburin shawarwari, don samun damar kyautata tsarin daidaita sabanin ra'ayi na kungiyar WTO."

Bayan da kasar Sin ta shiga cikin kungiyar WTO a shekarar 2001, ta yi kokarin kare ka'idojin kungiyar, da sa kaimi ga kokarin kyautata tsarin ciniki da ya shafi bangarori da yawa. Dangane da batun, Keith Rockwell ya yaba ma kasar Sin kan yadda take kokarin goyon bayan kungiyar WTO. A cewarsa, ba za a samu damar kulla wasu muhimman yarjejeniyoyi masu alaka da cinikin kasa da kasa ba, ba tare da gudunmowar da kasar Sin ke bayarwa ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China