in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Burundi na zargin Rwanda da sace wani masunci 'dan kasar
2017-06-22 11:17:48 cri

Rundunar 'yan sandan Burundi ta ce dakarun Rwanda, sun sace wani masunci 'dan kasar, a kogin Ruhwa na yankin Cibitoke dake kan iyakar kasashen biyu.

Kakakin rundunar 'yan sandan Pierre Nkurikiye, ya ce an sace masuncin mai suna Jackson Ndayikengurukiye ne jiya Laraba da misalin karfe 7:30 na safe.

Ya ce, dakarun na Rwanda sun harba harsasai biyar daga yankin iyakar kasarsu, al'amarin da ya tsorata masunta biyu dake kamun kifi a kogin Ruhwa, inda daya daga cikinsu, Jackson Ndayikengurukiye ya tsere zuwa bangaren Rwanda yayin da dayan kuma ya yi bangaren kasarsa wato Burundi.

A cewarsa, dakarun Rwanda sun kama tare da sace masunci da ya tsere zuwa bangaren kasarsu.

Pierre Nkurikiye ya ce, hukumomi daga kasashen biyu sun fara tattaunawa don ganin an mai da masuncin na Burundi a raye, yana mai cewa, al'ummar Burundi dake zaune a yankin kan iyakar kasashen biyu, sun ji karar harbin bindiga ranar Talata da misalin karfe 9:30 na dare.

Cikin 'yan watannin baya-bayan nan, sojojin Rwanda sun kashe sama da 'yan kasar Burundi 6, bayan sun zarge su da shiga yankunan kasarsu ba tare da ka'ida ba daga lardunan Cibitoke da kirundo na Burundi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China