in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi za ta yi zaben raba gardama kan gyaran kundin tsarinta a Mayu
2018-03-19 09:30:30 cri

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza, ya rattaba hannu a jiya, kan dokar da ta bayyana ranar 17 ga watan Mayun bana a matsayin ranar da za a gudanar da zaben raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar dake gabashin Afrika.

Dokar na da nufin gayyatar al'ummar kasar da suka yi ragista domin zaben raba gardamar da aka shirya yi a watan Mayun bana da kuma babban zaben shekarar 2020, da su je su kada kuri'a a ranar 17 ga watan Mayu.

Daftarin kundin tsarin na da nufin tsawaita wa'adin shugabancin kasar daga shekaru 5 da aka kayyade a shekarar 2005, zuwa shekaru 7, sannan zai ba da dama ga shugaban kasa ya yi wa'adi biyu a jere. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China