in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burundi ya nada kwamitin da zai gyara kundin mulkin kasa
2017-05-16 09:54:38 cri

Kakakin shugaban kasar Burundi Jean Claude Karerwa, ya ce shugaba Pierre Nkurunziza, ya kaddamar da wani kwamiti, wanda ya dorawa nauyin tsara sabon kundin mulkin kasa, a wani mataki na gyara kurakurai da aka fuskanta a baya.

Mr. Karerwa ya ce, a shekarar 2015 da ta gabata, Burundi ta ci karo da wasu matsaloli na gudanarwa, sakamakon gaza fahimtar wasu sassa na dokokin tsarin mulkin kasar.

Ya ce, kafa wannan kwamiti, zai kauda matsalolin da aka ci karo da su a baya, sai dai kuma wasu sassa ciki hadda jam'iyyun siyasa, da kungiyoyin fararen hula, da ma tsohon shugaban kasar Tanzaniya Benjamin Mkapa, wanda ke aikin shiga tsakani, na ganin kamata ya yi a gudanar da wannan aiki, bayan tattaunawar sulhu da aka tsara gudanarwa cikin wata Yuni mai zuwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China