in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NFF za ta duba rawar da Super Eagles ta taka a gasar cin kofin duniya
2018-07-02 10:21:52 cri

Hukumar kula da kwallon kafar Najeriya za ta sake bibiyar irin rawar da kungiyar wasan kwallon kafa ta Super Eagles ta taka a gasar da aka gudanar ta cin kofin duniya.

Wani jami'in hukumar kwallon kafan Najeriya ya fada a jiya Lahadi cewa, hukumar za ta yi taro kan Super Eagles wadda ita ce babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar, domin sake yin nazari kan yanayin wasan da kungiyar kwallon kafan ta Super Eagles take ciki a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 a kasar Rasha.

Bitrus Bewarang, shugaban kwamitin tsare tsaren hukumar kwallon kafan Najeriya (NFF), ya fadawa manema labarai cewa, har yanzu hukumar ba ta yi dubi kan yadda yanayin wasan na Eagles ya gudana a gasar cin kofin duniyar ba.

A cewarsa, wannan mataki zai baiwa hukumar kula da kwallon kafan kasar damar yin nazari game da kwazo da kuma raunin da tagawar 'yan wasan ke da su, da kuma duba irin matakan da za'a bi domin gano bakin zaren magance matsalolin a nan gaba.

Kungiyar wasan kwallon kafan Super Eagles ta sha kashi a wasanta na rukunin D a hannun Croatia da ci 2 da nema a wasanta na farko, yayin da ta lallasa Iceland da ci biyu da nema, sai kuma ta kasa kaiwa zagaye na gaba bayan da Argentina da doke ta da ci 2-1.

Shugaban kwamitin na NFF ya jaddada cewa, akwai bukatar horas da matasan 'yan wasa 'yan kasa da shekaru sha uku U-13 da kuma 'yan kasa da shekaru sha biyar U-15 a nan gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China