Ahmed Musa ya ce yana ganin cin Argentina ba abu ne mai wahala ba, inda ya ce suna sane cewa wasan da za su buga da Argentina na da muhimmanci, yana mai bayyana ta a matsayin na ko a mutu-ko-a-yi-rai.
Croatia ta samu maki 6 daga nasarori biyu da ta samu, inda za ta jagoranci rukunin, kuma idan Nijeriya ta samu damar doke Argentina, to za ta shiga jerin kasashe 16 da za su buga zagaye na 2 na gasar tare da Croatia, inda za su kora Argentina gida.
Dan wasan ya ce zai iya tunawa shekaru 4 da suka gabata, ya ci kwallaye 2 yayin da suke wasa da Argentina. Kuma da ya bugawa Leicester wasa a shekarar 2016, ya buga wasan sada zumunta da Barcelona inda Messi ke buga kwallo, kuma a nan ma ya zura kwallaye 2.
A don haka, ya ce a ganinsa, komai zai iya faruwa a wasa na gaba. Ya kara da cewa, abu mai yuwuwa ne ya kara shan wasu kwallayen 2. (Fa'iza Mustapha)