in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Croatia ta doke Najeriya da ci 2 da nema
2018-06-17 15:45:32 cri

Croatia ta fara buga wasannin ta da kafar dama, a wasannin gasar cin kofin duniya dake gudana yanzu haka a Rasha, inda a jiya Asabar ta samu nasara kan tawagar Super Eagles ta Najeriya da ci 2 da nema. Nasarar da Croatia ta samu dai ta sanya ta shigewa gaba a rukunin D, inda kuma Argentina da Iceland ke biye mata a wannan rukuni.

Croatia dai ta fito da 'yan wasa masu hazaka, wadanda a minti na 32 suka samu nasarar jefa kwallo a ragar Najeriya ta bugun kwana daga Modric wadda Rebic ya sarrafa, kana Mandzukic ya sanya wa kai. Dan wasan Najeriya Etebo ne ya sanyawa kwallon kafa nan take kuma ta fada ragar Super Eagles.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma Croatia ta kara kwallon ta biyu ta bugun daga kai sai mai tsaron gida, wadda kyaftin din kungiyar Modric ya zura a raga a minti na 71.

Croatia za ta buga wasan ta na gaba da Argentina a ranar 21 Yuni, kana Najeriya za ta kece reni da Iceland a ranar 22 ga wata duka dai a rukunin na D.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China