in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yaba da nasarorin da aka samu a Somalia cikin watanni 12 da suka wuce
2018-07-02 09:22:36 cri

Wakilin musammam na sakatare janar na MDD a Somalia, Micheal Keating, ya yabawa ci gaban da aka samu ta fuskar siyasa da tattalin arziki da tsaro da shugabanni a kasar suka cimma cikin watanni 12 da suka shude.

Micheal Keating, ya ce nasarorin da aka cimma sun ba Somalia damar kaucewa afkawa cikin matsananciyar yunwa tare da samun karin kudin shi da zartar da dokoki da kuma kyautata alakar aiki tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi.

Wata sanarwa da ya fitar, wadda ta taya al'umma da gwamnatin Somalia murnar cikar kasar shekaru 58 da samun 'yancin kai a jiya Lahadi, ta jinjinawa sauye-sauyen da aka yi ga tsarin mulkin kasar da dokokin zabe da kuma na bangaren tsaro.

Ya ce duk da wadannan nasarori, akwai sauran rina a kaba, yana mai kira da kada a rainawa kalubale, musammam mumunan tasirin tsattsauran ra'ayi da kuma hadarin da rikicin siyasa da sauran rikice-rikice za su yi kan ayyukan da za su amfani al'ummar kasar.

Ya kara da cewa, ajandar da gwamnatin ta tsara na da kyau, kuma tana bukatar hadin kan kasar da goyon bayan kasashen duniya.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China