in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya amince da kara wa'adin AMISON a Somaliya
2018-05-16 10:04:54 cri

A jiya Talata ne kwamitin sulhun MDD ya gabatar da wani kuduri na neman amincewa da karin wa'adi ga tawagar kungiyar tarayyar Afirka dake aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliya (AMISON)

Kudurin mai lamba 2415, wanda ya samu amincewar mambobin kwamitin su 15, ya kara wa'adin tawagar ta AMISON zuwa ranar 31 ga watan Yulin wannan shekara, zai kuma baiwa kwamitin damar nazarin rahoton da tawagar za ta gabatar masa.

A ranar 31 ga watan Mayun wannan shekara ce dai wa'adin aikin tawagar zai kare a Somaliya. Kwamitin sulhun MDDr dai na sa ran karbar rahoton hadin gwiwa na kungiyar tarayyar Afirka da MDD kafin ya yanke shawarar kara wa'adin tawagar ta AMISON.

Amma sai aka jinkirta kimanta aikin tawagar, inda ake sa ran karbar rahoton ranar 15 ga watan Yuni. Wannan al'amari ya tilastawa kwamitin sulhun sake canja ranar da tawagar za ta kammala aikinta a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China