in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha da Somalia sun bukaci a yi hadin gwiwa don yakar ayyukan ta'addanci
2018-06-17 16:37:48 cri

Shugabannin kasashen Habasha da Somaliya sun bukaci hadin gwiwar kasa da kasa domin yakar ayyukan ta'addanci wadanda suka haifar da hasarar rayukan al'umma a Somalia da ma sauran kasashen duniya.

Abiy Ahmed, firaiministan kasar Habasha da shugaban kasar Somalia Abdullahi Mohamed Farmaajo wanda ya karbi bakuncin Abiy, sun bayyana cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne ginshikan tabbatar da ci gaban dukkan kasashen, kuma dukkanninsu sun amince za su yi aiki tare domin yakar ayyukan ta'addanci, ciki har da tunkarar manyan kalubalolin tsaro dake addabar iyakokin kasashen nasu.

Abiy Ahmed wanda ya isa birnin Mogadishu domin ziyarar aiki ta kwana guda ya yabawa kokarin gwamnatin Somalia wajen magance kalubalolin tsaro da sauran batutuwan da suka shafi ci gaban kasar Somalia da dora kasar kan turbar dawwamamman zaman lafiya da ci gaba.

A wata sanarwar bayan taro ta hadin gwiwa da shugabannin biyu suka fitar a Mogadishu, sun bayyana gamsuwarsu game da rawar da dakarun wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika a Somalia wato AMISOM ke yi, wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Somalia, kana sun bukaci daukar dukkan matakan da za su tabbatar da dorewar zaman lafiya don gudun mayar da hannun agogo baya game da batun zaman lafiyar kasar Somalia.

Shugaba Farmaajo ya yi matukar yaba da irin sadaukarwar da AMISOM ta nuna, kana ya yaba da irin rawar da dakarun tsaron Habasha suka takawa wajen wanzar da zaman lafiyar a Somalia.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China