in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya da MDD sun sanya hannu kan shirin kasar na shekaru hudu
2017-12-06 10:24:41 cri

A jiya Talata ne, gwamnatin Somaliya da MDD suka sanya hannu kan wani shirin MDD na raya kasar ta Somliya cikin shekaru hudu masu zuwa mai suna UNSF a takaice.

Shi dai wannan shiri ya zayyana dabarun hadin gwiwa, matakan da hukumomin MDD 23 da tawagar MDD dake kasar ta Somaliya za su dauka wajen taimakawa manufofin raya kasar, kamar yadda aka zayyana a shirin raya kasar ta Somaliya da ma kokarin da kasar ke yi na cimma nasarar manufofin samun ci gaba mai dorewa.

MDD dai ta bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwa da ta fitar a birnin Mogadishu cewa, kulla shirin tsakanin sassan biyu, ya biyo bayan sakamakon da aka tattara ne, da shawarwarin da aka bayar, da fata da kuma yakinin da masu ruwa da tsaki suka nuna, ciki har da kungiyoyin fararen hular kasar, da kason kudaden da gwamnatin ke bayarwa gami da ra'ayoyin jama'a.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China