MDD ta bayyana a jiya Alhamis cewa, za ta kashe tsabar kudu har dala miliyan 12.3 a shekarar 2018 mai kamawa a wani mataki na kawar da matsalar yunwa a kasar Somaliya.
Jami'in dake kula da ofishin harkokin jin kai na MDD ko OCHA dake Somaliya Peter de Clerq shi ne ya sanar da hakan. Yana mai cewa, ofishin kula da harkokin jin kai na kasar Somaliya(SHF) ne zai sarrafa wadannan kudade gami da irin kudade da aka tara ta hanyar gudummawa domin taimakawa al'ummomin dake bukatar taimakon gaggawa.
Jami'in ya ce, za a yi amfani da kaso na biyu na kudaden asusun na SHF wajen taimakawa ayyukan yaki da yunwa guda 30 a wasu sassan kasar ta Somaliya da wannan matsala ta fi kamari. Ya ce, wadannan kudade za su baiwa abokan hulda a fannin ayyukan taimakon jin kai damar ci gaba da inganta matakansu na magance matsalar yunwa tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekara mai kamawa ta 2018.(Ibrahim)