in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta yi aiki tare da Somaliya don sake gina kasar
2017-10-25 09:24:06 cri

Jami'an MDD dake kasar Somaliya sun yi bikin ranar MDD a Mogadishu, babban birnin kasar, inda suka yi alkawarin cewa, za su ci gaba da ba da goyon bayansu ga kasar Somaliyan domin samun dawwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Da yake jawabi a wajen bikin, babban jami'in tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Somaliya ya nuna gamsuwa da irin goyon bayan da jami'an kasar Somaliyan ke baiwa MDD a kokarin da suke na taimakawa kasar.

Wakilin musamman na sakatare janar na MDD dake Somaliya Michael Keating, ya bukaci abokan aikinsa na MDD da su yi aiki tare da 'yan kasar ta Somaliya domin gina kasarsu, ya kara da cewa, kashe rayukan fararen hula masu yawa da aka yi a harin bam na ranar 14 ga watan Oktoba ba abu ne da za'a taba amincewa da shi ba.

Ana gudanar da ranar MDDr a ko wace shekara, domin tunawa da yarjejeniyar da ta kafa MDDr a shekarar 1945, bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China