in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Libya sun sanar da kwace iko da daukacin birnin Darna
2018-06-29 10:57:17 cri

A jiya ne kwamandan dake kula da sojojin dake gabashin kasar Libya Janar Khalifa Haftar, ya sanar da kwace iko da daukacin birnin Darna na gabashin kasar daga hannun mayaka masu tsattsauran ra'ayi.

Janar Haftar ya sanar da samun galabar ce a wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin, yana mai cewa, suna farin cikin 'yantar da daukacin birnin Darma bayan da dakarunsa suka yi nasarar fatattakar 'yan ta'adda da masu mara musu baya daga yankin.

Jami'in ya kuma bayyana godiya ga sojojin Libya da ma al'ummar Darna, kan yadda suka hada kai da sojojin a yakin 'yantar da birnin daga hannun 'yan ta'adda. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China