Masu tsaron gabar tekun Libya a ranar Lahadi sun yi nasarar ceton bakin haure ta barauniyar hanya kimanin 260 daga nahiyoyin Afrika da Asiya a yammacin gabar tekun Libya.
Kakakin dakarun tsaron ya ce, jami'an sun yi nasarar ceton bakin haure kimanin 180 da suka fito daga shiyyar Afrika da Asiya a cikin wasu kwale kwale na roba guda biyu a wani waje mai tazarar kilomita 36 daga birnin Garrabulli, wanda ke da nisan kilomita 60 daga Tripoli, babban birnin kasar, kakakin dakarun tsaron, Ayob Qassem ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Qassem ya kara da cewa, an kwashe wadanda aka ceto din zuwa sansanin sojojin ruwa dake Tripoli, kana an samar musu da tallafin jin kai da magunguna, sannan an mika su ga hukumar samar da matsugunai ta Tripoli a gaban wasu kungiyoyin kasa da kasa.(Ahmad Fagam)