in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu tsaron gabar ruwan Libya sun ceto 'yan ci rani 406 a kusa da yammacin gabar
2018-05-08 09:31:20 cri

Masu tsaron gabar tekun Libya sun ceto wasu 'yan ci rani 406, 'yan asalin nahiyar Asiya da Afrika, a kusa da yammacin gabar tekun kasar.

Kakakin rundunar sojin ruwan kasar Ayob Qassem, ya ce wasu jami'ai biyu dake sintiri ne suka ceto 'yan ci ranin cikin kwale kwalen roba guda 3 marasa kyau, a wani wuri mai nisan mil 25 daga gabar Garrabulli, wanda ke da nisan kilomita 55 daga gabashin birnin Tripoli.

Ayob Qassem ya ce, daga cikin mutanen da aka ceto, akwai mata 70 da yara 22, kuma an mika dukaninsu ofishin yaki da bakin haure dake Tripoli.

Ana yawan samun kwararar bakin haure daga Libya zuwa yankunan Turai a lokacin da aka samu kyan yanayi, musammam a bangaren yammacin tekun kasar.

Dubban 'yan ci rani ne ke zabar tsallake tekun Bahar Rum a yunkurinsu na zuwa Turai daga Libya, saboda yanayin rikici da ake fama da shi a kasar tun daga shekarar 2011.

Wata kididdiga daga ofishin yaki da bakin haure na kasar ta ce, adadin 'yan ci rani da aka ceto a tekun Libya cikin rubu'in farko na bana, ya haura 4,000. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China