in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara tattaunawa kan barazanar tsaron yankin Sahel a Morocco
2017-11-02 10:06:07 cri

A ranar Laraba ministan harkokin wajen Morocco Naser Bourita, ya tattauna da sakatare janar na kungiyar kasashen dake yankin kudu da hamadar Sahara wato CEN-SAD, Ibrahim Sani Abani, dangane da batun barazanar tabarbarewar tsaro a yankin Sahel.

Bangarorin biyu sun nuna damuwa dangane da yawaitar matsalolin kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma karuwar aikata muggan laifuka na kasa da kasa a wannan yankin.

Sakamakon tattaunawar, Abani ya shedawa 'yan jaridu cewa, akwai matsananciyar bukata na kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen dake yankin domin dakile wannan mummunar barazana.

CEN-SAD, wata hadaddiyar kungiya ce wadda aka kafa ta don tabbatar da hadin gwiwa wajen raya tattalin arziki ta hanyar aiwatar da dabarun gina ci gaban kasashen da lamarin ya shafa.

Mambobin kasashen kungiyar CEN-SAD su ne Benin, Burkina Faso, jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Chad, Comoros, Cote d'Ivoire, Djibouti, Masar, Eritrea, Gambia, Ghana, Guinea-Bissau, Libya, Mali, Mauritania, Morocco, Niger, Nigeria, Senegal, Saliyo, Somalia, Sudan, Togo da kuma Tunisiya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China