in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Sin zai gina gidaje dubu 2 ga 'yan sandan Zambiya
2015-10-28 11:08:49 cri

Shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu, ya fada a Talatar nan cewar, gwamnatin kasar ta baiwa kamfanin Avic International na kasar Sin kwangilar gina gidaje kimanin dubu 2 da 350 ga jami'an tsaron kasar.

Da yake jagorantar bikin kaddamar da ginin kashin farko na gidaje 48 ga jami'an 'yan sandan kasar a Lusaka, babban birnin kasar, Lungu, ya ce, yana fatan kamfanin zai kammala aikin nan da karshen watan Maris na shekarar badi.

Ya ce, aikin zai lashe kudi dalar Amurka miliyan 320, kuma idan aikin ya kamala, zai rage matsalar karancin muhalli da jami'an tsaron ke fama da shi.

Shugaban na Zambiya ya ce, matsalar karancin gidajen kwana na daya daga cikin manyan kalubalen dake damun kasar, don haka ya sha alwashin cewar, gwamnatin kasarsa za ta bullo da tsarin samar da gidaje masu kyau ga al'ummar kasar.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Davies Mwila, ya ce, karkashin shirin, za'a samar da gidaje 1,454 ne ga jami'an 'yan sanda, sai gidaje 677 ga jami'an kula da gidajen yari, sai gidaje 117 ga jami'an shigi da fici, sai kuma gidaje 102 ga jami'an hukumar hana sha da fasa kaurin miyagun kwayoyi.

Mataimakin shugaban kamfanin na AVIC International Gong Jiayan, ya ce, kamfanin zai gina ingantattun gidaje, kuma za'a kammala aikin cikin wa'adin da aka cimma matsaya kansa, samnan za su dau ma'aikata 'yan asalin kasar domin su samu aikin yi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China