Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana a yau Litinin, da Firaministan Faransa Edouard Philippe a nan birnin Beijing, inda ya ce a shirye kasar Sin take, ta yi aiki da Faransa wajen kara bunkasa muhimmiyar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A cewar Xi Jinping, duniya a yanzu na fuskantar sauye-sauye masu sarkakiya, yana mai cewa kasar Sin ta shiryawa aiki da Faransa ta yadda dangantakarsu za ta ci gaba da zama abun misali ta fuskar mutuntawa da morar juna da musaya da koyo da koyarwa a tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)