in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya bayyana nasarorin da ya samu kwanaki 100 bayan ya kama aiki
2018-02-26 09:46:44 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, wanda ke gab da cika kwanaki 100 da hawa karagar mulki, ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, yana mai alkawarin samar da sauye- sauyen da za su inganta tattalin arzikin kasar.

Emmerson Mnangagwa wanda ya karbi mulki ne a ranar 24 ga watan Nuwamban bara, ya bayyana cikin wani sakon murya da ya wallafa jiya a kafar sada zumunta cewa, ayyukan dake gaba na bukatar gudunmuwar daga kowa da kowa. Inda ya ce, za a dauki lokaci kafin a fara cin gajiyar sauye-sauyen.

Shugaba Mnangagwa, ya ce gwamnati ta gabatar da kasafin kudi da ya rage duk wasu kashe-kashen kudi da ba a bukata, ciki har da wasu abubuwan alfarma da manyan jami'an gwamnati ke samu.

Sabuwar gwamnatin ta saukaka dokar da ta ba 'yan asalin kasar damar mallakar mafi yawan jarin bangarorin tattalin arziki, ta yadda za ta ba da damar zuba jari a bangarorin hakar azurfa da lu'u-lu'u, domin jan hankalin masu zuba jari na kai tsaye daga kasashen waje.

Kafin karbar mulki daga hannun Robert Mugabe, dokar na bukatar 'yan asalin kasar su mallakar mafi yawan hannayen jari a bangarorin tattalin arziki, abun da bai yi wa masu zuba jari na kasashen waje dadi ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China