in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da mataimakan shugaban Zimbabwe
2017-12-29 10:40:43 cri

An rantsar da Constantino Chiwenga, tsohon babban jami'in soji da tsohon 'dan siyasa Kembo Mohadi, a matsayin mataimakan shugaban kasar Zimbabwe a jiya Alhamis.

Babban jojin kasar Luke Malaba ne ya rantsar da shugabannin biyu a wani biki da aka yi a fadar gwamnatin kasar, biyo bayan nadin da shugaba Emmerson Mnangagwa ya yi musu.

Shugaba Mnangagwa ya karbi mulki daga tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ne a watan da ya gabata, inda ya lashi takobin farfado da tattalin arzikin kasar da yaki da cin hanci da rashawa da kuma samar da aikin yi ga al'umma.

Constantino Chiwenga, shi ne ya jagoranci sojojin da suka sanya Robert Mugabe yin murabus, kuma yana daga cikin shugabannin soji da shuagaba Mnangagwa ya ba mukaman gwamnati.

Sauran sun hada da tsohon babban hafsan sojin sama Perrence Shiri wanda a yanzu ke zaman ministan kula da filaye da harkokin noma da kuma Manjo Janar Sibusiso Moyo mai ritaya, wanda yanzu ke matsayin ministan harkokin wajen kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China