in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe 'yan banga biyar a Najeriya
2018-05-16 09:39:47 cri

Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya (NEMA) ta sanar da cewa, wasu 'yan banga biyar sun rasa rayukansu, wasu biyar kuma suka jikkata, bayan da wani abu ya fashe a wani shingen binciken ababan hawa na soja a wajen garin Konduga na jihar Bornon arewacin Najeriya.

Hukumar NEMA ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yan bangan dai suna taimakawa sojoji ne a yakin da ake yi da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Fashewar dai ta faru ne, lokacin da jami'an tsaro suka dakatar da wani 'dan kunar bakin wake a shingen binciken ababan hawa dake mashigar garin na Konduga a jiya Talata da rana.

Mazauna garin Konduga dai, galibinsu manoma sun sha fama da hare-haren kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram. Ko da a watan Fabrairun wannan shekara ma, mutane a kalla 22 ne suka gamu da ajalinsu, baya ga wasu mutane 28 da suka jikkata sakamakon wasu hare-haren kunar bakin wake da mayakan kungiyar suka kaddamar a kasuwar garin na Konduga.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China