Ana gudanar da taron manyan jami'ai na kwamitin kula da harkokin amfani da sararin samaniya na MDD a Austria, inda aka zartas da wata takarda. A karo na farko an tsai da kudurin yin amfani da sararin samaniya cikin kwanciyar hankali.
Game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kudurin ya dace da bukatun bil Adama, wajen gudanar da harkokin dake da nasaba da sararin samaniya, wanda hakan ne burin al'ummun kasashen duniya baki daya.
Jami'in ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan kara kokari tare da sauran kasashe, ta yadda za ta kara taka rawar gani a wannan fannin.(Jamila)