in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD:Yanayin da ake ciki a Darfur na Sudan ta Kudu ya inganta
2018-06-12 09:35:29 cri

Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da ayyukan samar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, ya bayyana cewa, al'amura sun inganta matuka a yankin Darfur na kasar Sudan ta Kudu, a don haka wajibi ne tawagar dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin ita ma ta kara kaimi don kare rayukan mazauna wurin.

Jami'in ya bayyana hakan ne lokacin da yake yiwa zaman kwamitin sulhun MDD karin haske game da rahoton tawagar UNAMID, yana mai cewa, al'amura sun canja sosai a yankin na Darfur. Ya ce, fadan da ake tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyin 'yan tawaye ya takaita ne a sassan tsaunukan Jebel Marra.

A don haka, ya ce lokaci ya yi da MDD da kungiyar tarayyar Afirka AU za su tsara matakan goyon bayan da za su baiwa yankin na Darfur a nan gaba, ta yadda tawagar za ta ci gaba da aikin samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China