Rundunar sojin saman Nijeriya ta tabbatar da cewa. an kashe wani sojanta, biyo bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai wajen saukar jirgi mai saukar ungulu na rundunar a birnin Yenegoa na jihar Bayelsa mai arzikin man fetur dake kudancin kasar.
A cewar kakakin rundunar Olatokunbo Adesanya, jami'an tsaro sun mai da martani kan harin na ranar Lahadi da aka kai yankin Igbodene dake birnin.
Olatokunbo Adesanya ya kara da cewa, an fara bincike don gano musababbin harin.
Tsageru a yankin Neja-Delta na Nijeriya sun shafe shekaru da dama, suna fafutukar ganin sun karbe iko da mafi yawan albarkatun yankin.
Tsegerun dai na shan arangama da jami'an tsaro da aka tura yankin domin dakile ayyuknsu. (Fa'iza Mustapha)