Tunanin watsa labaru na Xi Jinping muhimmin kashi ne na tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki. Bayan taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18, Xi Jinping ya gabatar da sabbin ra'ayoyi da shawarwari da bukatu kan yadda za a kyautata aikin watsa labaru na jam'iyyar. Ya kuma amsa wasu tambayoyi a wannan fanni, da bayyana manyan batutuwan watsa labaru a fannonin matsayinsa a tarihi, alhakinsa, ka'idojinsa da sauransu, ta haka an kafa tsarin tunanin watsa labaru mai dacewa. (Zainab)