

A jiya Alhamis ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi tattaunawa da takwaransa na kasar Kazakhtan Nursultan Nazarbayev a nan birnin Beijing, inda suka kuma amince su karfafa dadadden zumuncin dake tsakaninsu, za kuma su yi aiki tare don ci gaba da daga martabar kasashensu. (Ibrahim)