in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta kafa kwamitin tafiyar da harkokin wasannin kwallon kafa na wucin gadi
2018-06-14 09:58:37 cri

Gwamnatin kasar Ghana ta kafa kwamitin wucin gadi mai mutane 5 domin duba yadda za'a tafiyar da harkokin wasannin kwallon kafa da sauran batutuwa dake da alaka da harkokin wasannin kasar, Mustapha Abdul-Hamid, ministan watsa labaran kasar ne ya tabbatar da hakan a jiya Laraba.

Mambobin kwamitin sun hada da Kofi Amoah, wani hamshakin dan kasuwa kuma mai sha'awar wasannin kwallon kafa, da Cudjoe Fianoo, shugaban gamayyar kungiyoyin wasannin kwallon kafa na kasar Ghana (GHALCA), da Abedi Pele, wanda ya taba rike matsayin fitaccen dan wasan Afrika har sau uku, Osei Kofi, tsohon dan wasan kungiyar Black Stars, da babban dan wasan babbar kungiyar kwallon kafan kasar da Eva Otchere, tsohon mai gabatar da labaran wasanni kuma lauya.

Sanarwar ta ce, gwamnatin Ghana za ta ci gaba da yin aiki tare da hukumar FIFA da kuma hukumar shirya wasannin kwallon kafa ta Afrika (CAF) domin tattauna irin cigaban da aka samu na baya bayan nan a wajen tafiyar da harkokin wasannin kwallon kafa na kasar, da kuma tattauna yadda za'a kai mataki na gaba tun bayan bayyanar bidiyon binciken badakalar cin hanci wanda dan jaridar nan na kasar Anas Aremeyaw Anas da 'yan tawagarsa suka bankado.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China