in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana za ta zurfafa binciken wurare dake da albarkatun mai a kasar
2018-03-22 10:41:03 cri

Wani jami'in kasar Ghana ya jaddada cewa, kasar za ta ci gaba da zurfafa aikin binciken danyen mai a yankunan kan kasa da na cikin tekun kasar.

Da yake gabatar da jawabi a yayin bude taron karawa juna sani game da dabarun kyautata ci gaban tattalin arziki da kasuwanci na kasar Ghana na shekarar 2018, ministan makamashin kasar Boakye Agyarko ya ce, ya zama wajibi su yi hasashen dukkan hanyoyin dake rage tasirin rawar da albarkatun mai da iskar gas ke takawa wajen ci gaban kasar a nan gaba.

Ministan ya ce, kasar Ghana tana da wasu wurare masu yawa wadanda ake sa ran akwai dunbun albarkatun mai da iskar gas dake jibge a yankunan. Daga cikin wuraren tekunan wadanda girmansu ya kai murabbin kilomita 256,000, daga cikin wuraren kashi 30 bisa 100 ne kadai aka gudanar da aikin binciko albarkatun man.

Amma game da wannan batu, Agyarko ya ce, abu ne mai matukar muhimmanci a sake fasalin kamfanin mai mallakin gwamnatin na kasar, kamfanin samar da mai na kasar Ghanan (GNPC), shi ne ke da alhakin tafiyar da harkokin man kasar wanda ya kunshi binciko man da kuma tattalinsa.

Alex Mould, tsohon babban jami'in kamfanin man na GNPC ya bayyana cewa, kamfanin man na GNPC shi ne kadai ke da ikon binciko albarkatun man, ya ce hakan na nufin cewa, idan wani kamfanin mai na kasar waje yana son gudanar da binciken danyen mai a Ghana, dole ne ya gudanar da aikin cikin hadin gwiwa da kamfanin na GNPC.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China