in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta shirya tunkarar barazanar ta'addanci
2018-01-18 09:53:05 cri

Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana ya bayyana cewa, babu wata matsalar tsaro a kasarsa, duk da hare-haren ta'addancin da ake kaiwa a kasashen dake makwabtaka da ita.

Shugaba Addo wanda ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, yayin bikin cika shekara guda a kan karagar mulki, ya ce, a zahiri ba za a iya tsame Ghana daga fuskantar hare-haren 'yan ta'adda ba, wannan shi ya sa mahukuntan kasar suka ba da muhimmanci ga daukar matakan tsaro.

Ya ce, idan aka kwatanta Ghana da yawancin kasashe dake shiyyar, hakika akwai kwanciyar hankali da tsaro a kasar, don haka za su kara daukar matakan da suka dace na ganin an ci gaba da kare martabar kasar Ghana a idon duniya.

Shugaban yana ba da wannan tabbaci ne kwanaki uku bayan da 'yan sanda suka kwace wasu abubuwa a Accra,bbabban birnin kasar, wadanda aka yi imanin cewa, abubuwan fashewa.

Taron manema labaran wanda shi ne na biyu tun lokacin da shugaba Akufo-Addo ya kama aiki a ranar 7 ga watan Janairun shekarar 2017, ya samu halartar wasu editoci da 'yan jaridu da aka zabo daga kafofin watsa labarai daban-daban na kasar, inda suka yiwa shugaban tambayoyi game da ayyukan da ya gudanar da kuma halin da kasar ke ciki a shekara dayan da ta gabata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China