in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Mutane 9 sun rasu a harin jihar Taraba
2018-05-10 09:12:54 cri

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da rasuwar mutane 9, yayin wani harin da aka kaiwa wasu mutane dake hanyar su ta zuwa majami'a a yankin Tutuwa dake karamar hukumar Ussa ta jihar Taraba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar David Misal, ya ce baya ga wadanda suka rasu, wasu mutane 3 kuma sun samu raukuna, baya ga wasu 2 da har yanzu ba a gan su ba.

'Yan bindigar dai, a cewar sifeton 'yan sandan Ussa Rimansikwe Karma, sun yiwa masu ibadar kwantan bauna ne a kan hanyar su da zuwa coci, suka kuma bude musu wuta, kana suka tsere kafin zuwan jami'an tsaro.

Ko da a ranar 8 ga watan Janairu ma dai wasu mutanen a kalla 12 sun rasa rayukan su, a wani hari na kisan ramuwar gayya da sassan mabiya manyan addinan yankin biyu ke wa junan su a jihar.

Jihar Taraba dai na fama da tashe tashen hankula masu nasaba da neman ikon filaye, da na banbancin addini da kuma kabilanci, lamarin da ya haifar da kisan dubban al'umma a 'yan shekarun baya bayan nan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China