in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Malawi ya gyayyaci kamfanonin Sin da su zuba jari a kasarsa
2016-06-23 11:21:21 cri

Shugaban kasar Malawi Peter Mutharika ya yi kira a ranar Talata ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasarsa da kuma taimakawa wajen kara fitar da kayayyakinsu.

Malawi na kokari domin kawo sauyi na tallafin kasuwancin da take samu, in ji mista Mutharika a yayin dandalin zuba jari tsakanin Malawi da Sin da ya gudana a Lilongwe, babban birnin Malawi, wanda ya tattara shugabannin kamfanonin Malawi da na jihar Anhui ta kasar Sin fiye da 300.

Mista Mutharika ya nuna kasar Sin a matsayin daya daga cikin manyan abokai na kwarai da abokan huldar kasuwanci na Malawi.

Ya kamata mu samar da kayyayaki da fitar da su daga bangarori da dama, in ji shugaban. Dangane da haka, muna gayyatar zuba jarin kai tsaye a bangaren noma da masana'antu, makamashi, hakar ma'adinai, fasahohin TIC, yawon bude ido, ababen more rayuwa da kere kere, da sauransu. Kun zo a daidai lokaci na tarihinmu, in ji shugaban Malawi.

Mista Mutharika ya bayyana cewa, Malawi wani wurin zuba jari mai kyau a kudancin Afrika, kuma masu zuba jarin kasar Sin za su ganin kasar a matsayin wani wurin da ya dace domin gudanar da harkokinsu na kasuwanci.

A cikin jawabinsa, shugaban tawagar kasuwanci ta kasar Sin Song Weipin, ya bayyana cewa, jihar Anhui ta kasar Sin ta kafa kamfanoni 23 a Afrika tare da zuba jari na dalar Amurka biliyan 1,2 a nahiyar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China