in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Malawi ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin
2016-02-01 10:35:23 cri

Shugaban kasar Malawi Bingu wa Mutharika, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a jiya Lahadi a birnin Lilongwe.

Da yake tsokaci yayin ganawar tasu, Mr. Mutharika ya bayyana cewa, a cikin shekaru 8 da suka wuce tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Malawi da Sin, huldarsu ta samu ci gaba sosai. Kaza lika kasar Sin babbar kawa ce ga kasar Malawi, tana kuma ba da babbar gundummawa a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwa, da aikin gona, da Ilimi, da tsaron kasar ta Malawi.

Shugaba Mutharika ya kara da cewa, an cimma babbar nasara wajen gudanar da taron koli na birnin Johannesburg, karkashin dandalin tattaunawa na hadin gwiwar Sin da Afrika, kuma shirye-shiryen hadin gwiwa da shugaban Sin Xi Jinping ya gabatar game da manyan fannoni 10 tsakanin Sin da Afrika, sun dace da shirin farfado da Afrika wanda kungiyar AU ta tsara. A daya bangaren kasar Malawi tana fatan ci gaba da gudanar da hadin gwiwa tare da kasar Sin, a fannonin kafa tashoshin samar da wutar lantarki, da gina filayen jirgin sama, da hanyoyi, da kuma sauransu, domin neman samun bunkasuwa.

Bugu da kari kasar Malawi za ta ci gaba da nacewa ga manufar kasancewar Sin kasa daya tak, tare da ci gaba da nuna goyon baya ga kudurin dunkulewar ta.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, isar da gaisuwar shugaba Xi yayi ga jagoran kasar ta Malawi. Ya kuma kara da cewa, an samu sakamako masu kyau, tun bayan da kasashen Sin da Malawi suka kulla huldar diplomasiyya, wanda hakan ya dace da babbar moriyar jama'ar kasashen biyu. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China