in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta damu da yanayi a Malawi gabanin babban zaben kasar na badi
2018-05-10 09:49:11 cri

MDD ta nuna damuwa game da yanayin rashin kwanciyar hankali da ake fuskanta a kasar Malawi, kimanin watanni 12 kafin babban zaben kasar na shekara mai zuwa.

Wata sanarwa da jami'ar MDD ta kasar ta Malawi Maria Jose Torres ta fitar, ta bayyana damuwar MDDr game da halin da ake ciki a kasar. Sanarwar ta buga misali da yadda aka tozarta wani dan jarida mai daukar hotuna, yayin da shugaban kasar Peter Mutharika ke gabatar da jawabin kaddamar da kasafin kudin kasar na shekarar 2018 zuwa 2019, a zauren majalissar dokokin kasar a ranar Juma'a.

MDD ta bukaci a gudanar da bincike, tare da hukunta wadanda suka aikata cin zarafin dan jaridar, tare da wasu mambobin majalissar dokokin kasar su 2, wadanda su ma suka fuskanci muzgunawa.

Kaza lika MDD ta jaddada muhimmancin martaba 'yancin bil Adama, na bayyana ra'ayi da ikon shiga kungiyoyi, ko harkokin siyasa ba tare da nuna banbancin jinsi ba. Har ila yau MDDr ta yi kira ga mahukuntan kasar da su kara azama, wajen tabbatar da nasarar gudanar babban zaben kasar dake tafe cikin lumana.

Tuni dai fadar shugaba Mutharika da ofishin mataimakin sa Saulos Chilima, suka fitar da sanarwa dake nuna takaicin abun da ya faru, suna masu neman afuwar wadanda al'amarin ya shafa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China