in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Taron SCO#Xi Jinping: SCO ta kafa sabon tsarin hadin kai a tsakanin shiyya-shiyya
2018-06-10 12:00:30 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Lahadi ya bayyana cewa, kungiyar SCO ta samu babbar nasara a cikin shekaru 17 tun bayan kafuwarta. Kasashe mambobin kungiyar suna bin tsarin dokar SCO, da yarjejeniyar hadin kai irin ta zaman jituwa da makwabtaka tsakanin kasashe mambobin SCO, don kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare na kafa tsarin kawance da juna, da rashin adawa da juna, da kin daukar matakai kan wani bangare. Xi ya yaba da irin manyan kirkire-kirkiren da aka samu kan manufofi da kuma aiwatawar da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, kana ya kafa wani sabon tsarin hadin kai na shiyya-shiyya, kungiyar dai na bada sabon tallafi ga zaman lafiya da bunkasuwar shiyya-shiyya. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China