in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Taron SCO#An yi shawarwari da bangarori daban-daban a wajen taron kolin Qingdao na kungiyar SCO
2018-06-10 11:26:58 cri
Bayan kammala taron shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi da takwarorinsa na kasashe membobin kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO a yau da safe, an fara gudanar da shawarwari wanda ya kunshi bangarori daban-daban a wajen taron koli na Qingdao. Shugaba Xi Jinping ne ya jagoranci taron shawarwari, inda ya gabatar da muhimmin jawabi.

Taron kolin Qingdao ya zama irinsa na farko tun bayan da kungiyar SCO ta kara adadin yawan membobinta, inda wakilai daga kasashe 'yan kallo da suka hada da Afghanistan, Belarus, Iran, Mongoliya da kuma wakilan MDD da sauran wasu kungiyoyin kasa da kasa suka halarci taron shawarwarin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China