in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Taron SCO#Taron kolin kungiyar SCO na da ma'anar tarihi, in ji Xi Jinping
2018-06-10 10:18:30 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Lahadi cewa, taron kolin kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO wanda ake gudanarwa a birnin Qingdao ya zama irinsa na farko da dukkanin shugabanni kasashe membobin takwas na kungiyar suka hallara, tun bayan da aka kara adadin yawan membobin kungiyar, al'amarin dake da ma'ana a tarihi. Sakamakon ingantuwar karfin kungiyar SCO, jama'ar kasashen yankin gami da kasashen duniya daban-daban na kara maida hankali da bayyana fatansu game da ayyukan kungiyar, kana kungiyar na cigaba da daukar nauyin da ya rataya a wuyanta a fannonin wanzar da zaman lafiya, da neman ci gaba, da samar da kyakkyawar makoma a wannan yankin. Kasar Sin na son yin kokari tare da sauran membobin kungiyar don tattara irin nasarorin da suka samu, da yin nazarin game da yanayin da ake ciki a sassan duniya, da kuma neman samun dauwamammen ci gaban harkokin kungiyar.(Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China