in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya sanar da 12 ga Yuni ranar demokaradiyya a kasar
2018-06-07 13:10:33 cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar da kasar za ta dinga gudanar da bikin ranar demokaradiyya.

Shugaba Buhari ya ce, zaben da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993, shi ne zabe mafi inganci da tsabta wanda aka gudanar cikin kwanciyar hankali tun bayan da Najeriyar ta samu 'yancin kanta.

Domin tunawa da wannan rana, shugaban ya kara da cewa, a ranar Talata 12 ga watan Yunin shekarar 2018, za'a gudanar da bikin a karon farko, daga wannan lokacin kuma za'a maye gurbin ranar 29 ga watan Mayun wanda ake warewa a matsayin ranar hutu domin gudanar da bikin ranar demokaradiyyar.

Abiola, shi ne wanda ya lashe zaben shugabancin kasar na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993, ya rasu a sanadiyyar bugun zuciya a lokacin wata ganawa da wasu jami'an kasar Amurka da suke tattaunawa game da sako shi daga gidan kaso bayan shafe shekaru 4 yana tsare.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China