in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadarin mota ya hallaka mutane 20 a jihar Ondo dake kudancin Najeriya
2018-05-30 20:43:52 cri

A kalla mutane 20 ne suka gamu da ajalin su, sakamakon wani hadarin mota da ya rutsa da su a jihar Ondo dake kudu maso yammacin Najeriya.

Jaridar Guardian ta kasar ta bayyana cewa, fasinjojin dake cikin wata mota kirar bas mai cin mutane 14, da na wata motar kirar Range Rover SUV sun kone kurmus, bayan da motocin biyu suka yi tawo mu gama da juna kuma nan take motocin da suke ciki suka kama da wuta.

An ce hadarin na jiya Talata, ya sabbaba hallakar dukkanin mutanen dake cikin motocin biyu, in ban da direbobin su da ke cikin halin matsananciyar jinya.

Rundunar 'yan sandan yankin da hadarin ya auku, ta ce hadarin ya auku ne sakamakon tukin ganganci. Da ya ke tsokaci game da hakan, kakakin hukumar 'yan sandan Femi Joseph, ya ce daya daga direbobin motocin biyu na kokarin wuce wata mota ce dake gaban sa, lokacin da wadda ke tahowa daga daya bangaren ta nufo, nan take kuma suka yi karo na gaba da gaba.

Kaza lika wata majiyar ta daban ta ce, cikin mutanen da suka rasu, hadda wadanda ba sa cikin motocin da suka yi karon.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China