in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka 'yan bindiga 68 a arewa maso yammacin Najeriya
2018-05-23 09:37:06 cri

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan 'yan bindiga kimanin 68 da kuma raunata wasu a yayin arangama tsakanin jami'anta da mayakan a jihar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Udeagbala Kennedy, kwamandan rundunar sojojin Najeriya a jihar Sokoto, ya shedawa 'yan jaridu a Gusau, babban birnin jihar Zamfara cewa, an kama wasu mutane shida da ake zargin masu yin garkuwa da mutane ne, sai dai ya ce sojoji 2 sun rasa ransu a lokacin arangama da 'yan bindigar.

Ya ce 'yan bindigar sun kaddamar da hare hare a kauyukan Birane da Bawar-Daji a watannin Fabrairu da Afrilu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 64.

Kennedy ya ce, rundunar sojojin Najeriyar da sauran hukumomin tsaro sun fara aikin tarwatsa dukkan maboyar 'yan bindigar da kuma kawo karshe ayyukan maharan a fadin jihar.

Maharan sun kaddamar da hare hare masu yawa a jihar tun a farkon wannan shekarar, duk da irin namijin kokarin da gwamnatin shugaba Buhari ke yi na shawo kan matsalar.

A kwanakin baya be shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Zamfara, inda ya gana da shugabannin gargajiya da na al'umma domin tattauna yadda za'a shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China