in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: An kammala taron jawo ra'ayin masu zuba jari
2018-05-24 09:23:18 cri

A jiya Laraba ne aka kammala taron janyo hankulan masu zuba jari a sassan tattalin arzikin Najeriya, taron da aka fara tun a ranar Talatar farkon mako.

Mahukuntan kasar dai sun ce, taron mai taken "Zuba jari mai tattare da dunbin riba", na da manufar sada masu sha'awar zuba jari na cikin gida da na ketare da damammaki, na shiga hada hada a sassa daban daban a fagen raya tattalin arzikin kasar, ta yadda su ma za su ci gajiya daga riba mai tarin yawa.

Taron wanda ya gudana a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, ya samu halartar sassan masu zuba jari kimanin 200, daga kasashen duniya 14 na nahiyoyi 4, kuma hukumar bunkasa hada hadar zuba jari ta kasar ce ta shirya shi.

Kaza lika gwamnatin Najeriyar ta gabatar da ayyukan zuba jari na kai tsaye guda 100 a sassa 7, domin masu sha'awar zuba jari su zabin wadanda suka dace da harkokin su. Hakan a cewar mahukuntan kasar zai baiwa wadanda suka halarci taron damar shiga a dama da su, a fannonin da suka kunshi raya noma da sufuri, da kere kere, da sarrafa kayayyaki, da lantarki da iskar gas, da kuma fannin fasahar sadarwa.

Da yake tsokaci yayin bude taron, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya ce Najeriya na da albarkatu masu tarin yawa, ciki hadda na bil Adama, wanda hakan ya sanya ta zama kan gaba a dukkanin fadin nahiyar Afirka.

Ya ce, tun bayan farfadowar kasar daga mummunan yanayin tattalin arziki, Najeriyar na matukar bukatar daukar matakan tada komada, domin murmurewa daga gibin tattalin arziki da ta fuskanta a baya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China