in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin saman sojin Algeria ya kauce hanya, babu hasarar rayuka
2018-06-04 09:57:37 cri

Ma'aikatar tsaron kasar Algeria ta tabbatar a cikin wata sanarwa cewa, wani jirgin sojin saman kasar ya kauce hanya a ranar Lahadi a lardin Biskra, mai tazarar kilomita 450 a kudancin Algiers, babban birnin kasar, inda mutane 8 suka samu raunuka.

Sanarwar ta ce, lamarin ya faru ne a daidai lokacin da jirgin saman sojin samfurin Hercules C-130 ke kokarin sauka, inda ya kaucewa titin saukar jiragen saman, daga wajen saukar jiragen a sansanin sojojin saman na Biskra, amma matuka jirgin sun samu kananan raunuka, inda aka ba su kulawar gaggawa, kana an samu hararar kayayyaki a sanadiyyar faruwar hadarin.

Sanarwar ta kara da cewa, tuni babban hafsan sojojin kasar ya bayar da umarnin a gudanar da bincike game da faruwar hadarin.

Wannan shi ne karo na biyu da aka samu hadarin jirgin sama a kasar cikin watanni biyu. Kasar ta arewacin Afrika ta gamu da mummunan ibtila'in hadarin jirgin sama a ranar 11 ga watan Afrilun wannan shekarar, wanda kuma shi ne hadarin jirgin sama mafi muni da kasar ta taba fuskanta, kamar yadda hukumar tsaron kasar ta tabbatar da cewa, hadarin jirgin saman na Ilyushin I-76 ya hallaka dukkan fasinjojin dake ciki wanda ya hada har da sojojin kasar da iyalansu 247, da kuma ma'aikatan jirgin su 10.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China