in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria ta kau da yiwuwar tura sojojin ta Libya da Mali
2018-01-23 10:29:42 cri

Ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Algeria Abdelkader Messahel, ya kau da duk wani zato na tura dakarun kasar sa zuwa kasashen Libya da Mali domin tallafawa yaki da ta'addanci.

Mr. Messahel ya ce, akwai dabaru daban daban na tallafawa kasashen kewayen Algeria dake yankin Sahel, ciki hadda samar da horo da sanin makamar aiki, kamar yadda kasar ta jima tana yi ga jami'an kasashen Mali da Nijar.

Messahel ya ce, cikin shekaru 10 da suka gabata, Algeria ta kashe kudi da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 100 wajen gudanar da tsare tsare, na ba da tallafin jin kai a aikin da ake yi, na dakile kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sahel, da ma sauran sassan masu kusanci da shi.

Ya ce, kasashen Libya da Mali ne kadai ke da alhakin kawo karshen tashe tashen hankula dake addabar su, duk da cewa a hannu guda Algeria na tallafawa da dabarun diflomasiyya, domin ganin an kai ga hawa teburin shawara a kasashen biyu.

Jami'in ya kara da cewa, tura sojoji daga wasu kasashe zuwa Libiya da Mali ba abun da zai haifar sai kara dagula al'amura a kasashen.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China