in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria ta yi kira a samar da  dabarar yaki da hanyoyin da 'yan ta'adda ke samun kudi
2018-04-10 09:13:14 cri

Algeria ta yi kira ga kasashen Afrika da su samar da wata dabara ta nahiyar, da za ta yi yaki da hanyoyi daban-daban da 'yan ta'adda ke samun kudi.

Ministan harkokin wajen Algeria Abelkader Messahel ne ya yi kiran, yayin wani taron manyan jami'ai kan yaki da hanyoyin da 'yan ta'adda ke samun kudi, wanda ya gudana jiya a birnin Algiers na Algeria.

Taron da Abdelkader Messahel ya jagoranta, ya mai da hankali ne kan tattauna kalubalen da ake fuskanta, dangane da kokarin da ake na tantance asalin hanyoyin da 'yan ta'adda ke samun kudi da nufin toshe su baki daya.

Da yake jawabin bude taron, ministan na Algeria, ya ce akwai hanyoyi 11 da 'yan ta'adda ke samun kudi da suka hada da safarar kwayoyi da na bil adama da yin garkuwa da mutane don karbar kudin fansa da safarar makamai da satar fasaha da roko da almundahana da kaura ba bisa ka'ida ba.

Abdelkader Messahel ya bukaci al'ummomin duniya su yi aiki tare wajen samar da nagartattun hanyoyin yaki da wadannan hanyoyi ta hanyar musayar bayanai da dabaru.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China